3 Satumba 2026 - 11:35
Source: Almanar
Kwamandan Sojojin Kasar Iran: Za Mu Kasance A Fage Da Karfi A Duk Inda Muradun Iran Ke Bukata

Kwamandan Sojojin Kasa na Iran, Birgediyar Janar "Ali Jahanshahi", a ziyarar gani da ido da ya kai kan rundunar yaƙi na rukunonin da ke aiki a yammacin Iran, ya jaddada cewa za su kasance a fagen da karfi a duk inda muradun Iran ke bukata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Janar Jahanshahi ya jaddada cewa rukunonin sojojin kasa na Iran suna cikin shiri na cikakken lokaci don fuskantar duk wata barazana da za ta iya faruwa a yankunan kan iyaka.

Ya kara da cewa sojojin kasa na Iran suna tsaye a kan iyakokin ƙasar, kuma za su kasance da cikakken ƙarfi a fagen duk inda tsaro da muradun Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bukatar kasancewa da karewa.

……………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha